An rufe kasuwar sayar da wayar salula (farm center) ta kano a yau

Jami an kotu bisa rakiyar Jami an tsaro sun rufe kasuwar farm center ta jihar kano.

Bayan da yan kasuwar ta farm center suka isa wajen sesuka tarar da duk Jami an kotu sun lika wata takarda dake dauke alamar cewa an rufe kasuwar sakamakon kasuwar ta zama mallakin wani mutum daya me suna Alhaji Muntari.

Alhaji Muntari wani mutum ne daya Dade ana rigima dashi a kotu akan cewa gabadaya filin kasuwar ta farm center mallakin Sa ne.

An tambayi yan kasuwar ta farm center game da wannan hukunci da suka wayi gari dashi, sesukace su ba asanar dasu hakan ba, ba a basu wani notice ba, sudai sunzo sun tarar an aiwatar da hukuncin ne kawai amma suna kira ga gwamnatin kano data shigo ciki.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *