Na Shiga Wani Yanayi Lokacin Da Na Karɓi Mulki Ina Da Shekara 30 – Gowon

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya ce ya shiga wani yanayi a lokacin da ya zama shugaban kasa a ranar 1 ga watan Agusta yana da shekaru 30.

Tsohon shugaban ya yi jawabin ne a wurin taron da aka yi ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti da gidauniyar ANISZA ta shirya.

Gidauniyar ta shirya taron ne don bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Gowon ya zama shugaban Najeriya mafi ƙarancin shekaru a lokacin da ya zama shugaba mukin soji a ranar 1 ga watan Agustan 1966 kafin ya cika shekaru 31 a ranar 19 ga watan Oktoba.

Ya yi mulki daga shekarar 1966 zuwa 1975.

“Na shiga sauyin yanayi a lokacin da na kama mulki a matsayin shugaban kasa. Ban taɓa tunanin zan zama shugaban ƙasa ba, abin ya faru ne kawai.”

Tsohon shugaban kasar ya tattauna da matasan Najeriya da suka hallarci taron ta fasahar intanet inda aka tattauna batutuwa da suka shafi zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya da ma duniya.

“Dattijon ya yi waiwaye kan wasu abubuwa da suka faru a rayuwarsa kuma ya bawa matasan shawarwari kan yadda za su gina kansu da ƙasa.

“Cikin mahalarta taron akwai wasu yara ƴan makaranta da ‘ya’yan ƙungiyar makarantar ANISZA da suka zaune kusa da wacce ta shirya taron mai suna Isioro yayin da ta ke tattaunawa da tsohon shugaban ƙasar.

“Gowon ya sake jaddada imaninsa game da hadin kan Najeriya inda ya ce za a iya zama lafiya duk da banbancin addini da kabila.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *