Marigayi Sardauna, Tafawa Balewa Da Aminu Kano, Sun Fara Gwagwarmayar Cigaban Arewa Tun Suna Matasa

……Yaushe matasan yankinmu zasu fara Gwagwarmayar kishin yankinmu na Arewa?

Rubutawa: Isah Abdullahi Dankane Gusau

Shin matasan Arewa munsan tun lokacin da Sardauna, Tafawa balewa da Aminu Kano suka fara gwagwarmaya akan Arewa?

Idan muka koma tarihi zamu ga sunfara gwagwarmaya ne
akan Arewa tun sunada karancin shekaru 20, 30, zuwa 35!!

To mufa yaushe zamu fara a matsayin mu na masu kishin Arewa!!

Aminci agareku yaku matasan Arewa, a matsayina na daya daga cikinku zanyi amfani da wannan dama na tunatar daku wasu muhimman abubuwa dasuke hakkine agaremu Amma mukeyin sakaci dasu.

Sanin kowa ne matasa sune ginshikin kowace al’umma domin kuwa sune iyaye Kuma shuwagabannin gobe.

Hakane ma yasa masana masu hangen nesa sukace duk al’ummar da matasan ta suka hada kai suka zama tsintsiya madaurinki daya to wannan al’umma zasu zama jagaba akowanne irin fanni na rayuwar yau da kullun.

Shikuma wannan hadin Kai bazaisamu a tsakanin mu ba harsai mundauki Arewa a dunkule ma’ana mudauki cewa Arewa maso gabas Arewa maso yamma Arewa ta tsakiya da duk wani yanki na Arewa a matsayin abu guda cewa duk abunda ya shafi kowane yanki na Arewa farinciki ne ko bakincine cewa Arewa yasha fa baki daya.

Babu shakka idan muka samu wannan to mundauko hanyar ci gaban Yankin mu na Arewa.

Mu kuma gamsu cewa zamu tallafawa junanmu Kuma zamu mutunta junanmu mu daure mutashi tsaye muyi karatu mu nemi sana’a.

Madogara: DAN AREWA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *