Kalaman Buhari: Ba Girin-Girin Ba Ta Yi Mai – Jega

Tsohon Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega yace abubuwan da Shugaban kasa Buhari ya fadi a jawabinsa na ranar yancin kai a kasa ya kamata a gansu ba wai ya tsaya a fatar baki ba kawai.

Jega ya yi wadannan kalamai ne lokacin da yake maida martani dangane da jawabin da shugaban kasa ya yi na ranar ‘yanci, a cikin wani shiri na musamman na gidan talbijin din Channels domin bikin cikar Najeriya shekaru 60.

“Abunda yake a bayyane shine cewa jawabin nasa na dauke da abubuwa da dama da suka dace a fade su a irin wannan rana.


“Ina ganin yana da matukar muhimmanci ayi magana kan abunda ya kamata gwamnati tayi domin tabbatar da ganin cewa a duk lokacin da aka yi kira ga ‘yan Najeriya don yin alfahari da Najeriya, sai ya zamana akwai wasu abubuwa da za su karfafa masu gwiwa da taimaka masu wajen aikata hakan.”

Yayin da ya yarda cewa Najeriya ta yi nisa a cikin shekaru 60 da suka shige, farfesan ya yi kira ga yin taka tsan-tsan, inda yace lallai bikin yancin kai na 60 ya zama lokaci na tunani. “Shakka babu a cewa Najeriya ta yi nisa a shekaru 60 da suka gabata, amma kuma yana da matukar muhimmanci kada a kasance a yanayi na biki, maimakon haka kamata yayi ayi amfani da lokacin a matsayin na tunani cikin tsanaki a kan abunda muke so Najeriya ta zama a shekaru 60 masu zuwa,”

Jega ya kara da cewar duk da kasar na fuskantar matsaloli da dama, ya kamata jawabin Buhari ya zaburar da wadanda ke kan mulki ta yadda za su yi abubuwan da zai karfafa wa al’umman kasar gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *