Zargin Ɓata Suna: Basaraken Zamfara Ya Maka Shugaban ‘Yan Sanda Kotu

Basarake Alhaji Abubakar Ibrahim, ya maka Shugaban ‘yan sanda na ƙasa Muhammed Adamu da wasu mutane 5 akan tsareshi ba bisa ka’ida ba da kuma bata masa suna.

Gwamnatin jihar Zamfara ta tube wa Ibrahim rawani shekarar da ta wuce, kuma ta adana shi a gidan gwamnati na tsawon watanni 11, sakamakon laifi taimakon ‘yan ta’addan da suka addabi jihar.

Sauran mutane 5 da Ibrahim ya maka a kotun sune DG na ‘yan sanda, CP na ‘yan sanda, AD na ‘yan sanda, DSS da sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Bala Maru.

Basaraken dai ya kai karar kotun tarayya dake Gusau, na neman Naira Biliyan 6.5 a hannun su sakamakon kama shi da suka yi ba bisa ka’ida ba, rike shi na wani lokaci da kuma bata masa suna a idon duniya.

Bayan Alkalin kotun, Fatima Aminu ta gama sauraron karar, ta maida karar babbar kotun jihar Zamfara don yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *