Zaɓen 2023: Inyamuri Za Mu Zaɓa – Ƙungiyar Yarbawa

Wata kungiyar Yarabawa mai suna IPSC a taƙaice, tayi kira akan a bar Inyamurai su mulka Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.

Kungiyar tace mulkin Najeriya a hannun Inyamurai zai kawo adalci, hadin kai da kuma ba wa kowa hakkinsa da dawo da zaman lafiya a tarayyar Najeriya.

Kungiyar ta Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, Daular Yarbawa ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023.

Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo.

IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya.

Ƙungiyar tace ayi amfani da NC na 2014, wanda yace kowanne dan kasa zai iya mulkar Najeriya.

A wani labari na daban, John Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa’a tun farkon shi.

A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Benin a ranar Litinin, ya ce ba don salon mulkin ba, da Najeriya ta samu cigaban da ya wuce na yanzu.

A yayin jajantawa a kan manyan kalubalen da suka addabi kasa, Oyegun ya ce wadanda ke mulki a yanzu ba su yin kokarin da ya dace kuma hakan ta sa ‘yan Najeriya suka sare. “Al’amura sun yi tsauri.

Abinda zan iya cewa shine an gina ginshikin cigabanmu amma kuma mulkin nan babu sa’a,”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *