Saura Ƙiris Boko Haram Ta Zama Tarihi – Buni


Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tabbacin cewa Boko Haram ta kusa zama tarihi a mulkin Buhari, kasancewar ‘yan ta’adda ba za su iya fin karfin shugabanni da mabiyansu ba.

Buni ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin jajantawa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, kan harin da Boko Haram ta kai wa tawagarsa a hanyar zuwa Baga.

“Abu daya da ‘yan ta’adda ba za su iya yi ba shine kawar da yakinin ku al’umar Borno, da ma sauran jihohi. Kuma ba za su iya kawar da kokarin gwamnati na kawo karshen su ba.”

Haka zalika, Gwamna Zulum ya gana iyalan ‘yan sanda da ‘yan sa kai JTF wadanda aka rutsa da su a harin da aka kaiwa tawagarsa ranar Juma’a, a hanyarsa ta zuwa Baga.

Ya ziyarci shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke a Maiduguri a ranar Litinin inda ya jajantawa iyalan wadanda harin ya salwantar da rayukansu da jikkata su.

A yayin ziyarar, kwamishinan ‘yan sanda, Bello Makwashi, ya zayyana sunayen jami’an rundunar da suka mutu sakamakon wannan hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *