Rt. Hon Abdullahi, Tare Da Hadin Guwar NCWD Ya Talafawa Mata Da Matasa 1000

Kimanin Mata da Matasa 1,000 daga mazaban Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu zasu ci gajiyar wannan talafi was ce hukumar cigaban da walwalar Mata wato (National Centre for Women Development) suka shirya.

A horar da Matan da Matasa a kan sana’o’i daban daban har na tsawon kwana Uku sannan sun karbi tallafi da kayan aiki a Ranar Alhamis 1st Octoba 2020 a Makarantar Central Primary School Kontagora, Niger State.

Mata da Matasan sun samu zimar samu horo a akan sana’o guda Shidda, Kama daga kiwon Kifi da kiwo Kaji da koyon yin Talalmi da Koyon dinki da saka awarwaro da kuma koyon yadda ake sarafa kayan abinci.

A jawabi Hon. Abdullahi Idris Garba a gurin taron, ya ce duk wadanda ake yayewa a yau sun samu horo ne akan “kiwon Kifi da kiwo Kaji da koyon yin Talalmi da Koyon dinki da saka awarwaro da sauransu, daga gwararun masu horar daga cibiyar kula da cigaban Mata ta kasa wato National Centre for Women Development.

Duk wadanda suka samu wannan horar kowanin su zai samu talafi da kayan aiki domin fara aiwatar da abinda suka koya domin inganta rayuwarsu.

Hon. Abdullahi ya Kara da cewa mutane 167 da suka samu horo a dinki zasu samu talafi kudi da keken dinki, wasu kuma zusu na’urar yin Talalmi wato shoe making machines, sannan mutane 166 daga ko wata gundumomin wato wards da ke karkashin mazabana traders who were selected da suka koyi yadda akr sarafa da Adana kayan abinci da Kudi domin bunkasa kasuwanci su.

Hon Abdullahi ya kara da cewa wannan shi ne talafi Mafi girma da aka yi a wannan kasa da ya kunshi abubuwan da Mata da Matasa zasu dogoro da kansu.

Idan kuka lura da kyau wannan cibiya ta cigaban Mata suna aiki tukuru domin ganinan rage talauci a tsakanin Mata da Matasa a fadin kasan domin cinma muradin Shugaba Buhari na rage yawan Mata da Matasa Matasa marasa aikin yi tare domin dogaro da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *