Shugaba Trump Da Uwargidansa Sun Kamu Da Korona

Medical workers in protective suits tend to coronavirus patients at the intensive care unit of a hospital in Wuhan, China.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kamu da COVID 19 da aka fi sani da Corona kimanin kwanaki 31 kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar.

Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko.

“A daren yau, ni da “FLOTUS mun kamu da COVID 19. Za mu killace kanmu ba tare da bata lokaci ba.

Za mu ci gallaba a kan wannan tare!” kamar yadda ya rubuta.

A kwanakin baya dai an ruwaito Shugaba Trump yana sukar yadda ake neman siyasantar da batun cutar ta CORONA zuwa ga wani abu na daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *