Katsina: Za A Bude Makarantu A Watan Gobe

Gwamnatin jihar Katsina ta ce makarantun gwamnati da masu zaman kansu na Firamare da sakandare za su koma karatu a ranar 5 ga watan Oktoban 2020.

Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal ne ya bada wannan sanarwar a ranar Talata a Katsina a tattaunawar shi da manema labarai.

Kwamishinan ya ce za a fara yi wa daliban bita don jarrabawar zango na biyu daga ranar 5 ga watan Oktoba zuwa 16 ga watan yayin da za a fara jarabawar zango na biyun daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Oktoba.

Lawal ya kara da cewa dalibai za su koma zangon karatu na uku daga 26 ga watan Oktoban 2020 zuwa 24 ga watan Janairun 2021 yayin da za a fara jarabawar zango na uku daga ranar 25 ga watan Janairu a kuma kammala ranar 5 ga watan Fabrairun 2021.

Ya ce dole dalibai da malamansu su rika saka takunkumin fuska a harabar makaranta su kuma rika bada tazara a tsakaninsu da kiyayye sauran dokokin dakile yaduwar COVID 19.

Ya kara da cewa gwamnati za ta yi feshin magunguna a makarantar sannan ta samar da abubuwan wanke hannu da na’urar gwada zafi/sanyin jiki don gane masu zazzabi mai zafi.

Har wa yau, kwamishinan ya ce za a raba daliban ne rukuni zuwa rukuni, ajin frimari daya zuwa uku za su zo makaranta daga karfe 7.30 na safe zuwa 12.30 na rana yayin da aji daya zuwa shida na frimari za su fara aiki daga 12.30 na ranar zuwa 5.30 na yamma.

Lawal ya yi bayanin cewa masu zuwa jeka ka dawo a makarantun sakandare da na kwana za su rika zuwa makaranta karfe 7.30 na safe su tashi zuwa 12.30 na rana ga wadanda ke bangaren karamar sakandare.

Wadanda ke sashin babban sakandare kuma za su shiga makaranta daga 12.30 na ranar su tashi karfe 5.30 na yamma a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *