Na Yi Dana Sanin Bincikar Magu – Salami

Tsohon Alkalin kotun daukaka kara, mai shari’a Ayo Salami ya koka da yadda ya jefa kansa a rikici bayan ya yi ritaya cikin kwanciyar hankali.

Wasu Lauyoyin da su ka zauna da Ayo Salami ne su ka bada wannan labari inda suka ce ” Ayo Salami ya yi nadamar karbar shugabancin kwamitin shugaban kasa na binciken tsohon shugaban hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu.

Wasu lauyoyi biyu su na wurin da tsohon Alkalin ya bayyana haka kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana a ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2020. Tsohon Alkalin babban kotun daukaka karar ya yi wannan kuka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya ke sauraron masu kare Ibrahim Magu. Wannan kwamiti na Ayo Salami ya na zama ne fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Jaridar premium times ta ce ”ana samun labarin wannan bincike ne daga lauyoyi da shaidun da su ka halarci zaman, bayan kiran a fadada masu zuwa zaman ya faskara. Wasu Lauyoyi biyu da su ka tsayawa tsohon shugaban EFCC, Magu, da su ka halarci zaman makon jiya, sun ce Salami yayi nadamar karbar wannan bincike.

Tosin Ojaoma da Zainab Abiola sun ce Ayo Salami ya fada masu kafin a soma zama cewa ya yi da-na-sanin amincewa da karbar shugabancin kwamitin. Lauyar Ibrahim Magu ta bada labari: “Duk mun zauna a matsayinmu na Lauyoyi, Alkali (Ayo Salami) ya ce ya yi nadamar aiki a kwamitin nan.”

Ta kara da cewa: “Mu na fara zama, Salami ya rika nuna nadama, inda ya dauko tsummar goge fuska ya ce ya na cike da da-na-sanin karbar wannan aiki.

” Da Abiola ta tambayi Lauyan ko cewa ya na wannan kuka ne a dalilin gaza samun Magu da wani laifi, sai ya cigaba da fadin abin da ya ke fada na nadama. Shi ma Ojaoma ya ce: “Salami ya yi ta cewa ya ji kunyar karbar wannan aiki. Ya koka da cewa ya yi ritaya, ya na zaune bai da wata damuwa, ya na cin tuwo da iyalan sa amman aka hadashi da rikici”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *