Allah Ya Yiwa Alkalin Alƙalai Na Jahar Kano Rasuwa

Allah ya yiwa tsohon babban alkalin jihar Kano, Mai Shari’a Shehu Atiku rasuwa, a ƙarshen makon nan da muke ciki.

Shehu Atiku ya rasu ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kakakin bangaren shari’a na jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Tuni aka yi jana’izar babban alkalin a yau Litinin, da karfe misalin ƙarfe 10:00 na safe, kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Marigayi Alƙali Shehu Atiku ya yi ritaya daga aiki a watan Janairun 2015.

Majiyoyi sun ce za a rika tunawa da marigayin saboda irin rawar ganin da ya taka a shari’ar wasu bankuna da suka durkushe duk da kokarin bashi toshiyar baki da suka yi.

Wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya shiga dimuwa kan rasuwar alkalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *