Yadda Ake Hada Kunun Aya Mai Kara Ruwan Maniyyi Da Namiji

Kayan Hadi

  • Aya
  • Kwakwa
  • Dabino
  • Sugar
  • Madara
  • Flavor
  • Citta
  • Kannun Fari

Yadda Za Ki Hada Kunun


Ki gyara ayarki ki cire duwatsu da dattin cikin sannan ki jika a ruwa ta yini ko ta kwana amma idan zata kwana ki tabbata cin canza ruwan gudun kada ta yi tsami, sannan ki cire kwallon cikin dabino ki jika dabinon, ki yayyanka kwakwarki kanana, idan kin zo markada wa sai ki zuba wanke ayar ki zuba a blender, ki zuba kwakwa da dabino a kai kiyi blending ko ki kai inji a markado miki ita, bayan kin markada sai ki tace da kyalle akalla sau biyu, sannan ki zuba sukari da flavor da kankara, idan anzo sha kuma sai a zuba madara ta ruwa ko ta gari.


Shi kunun aya baya son zafi da zaran yayi zafi to zata yi yauki, sai a bar ta a kankara ko a saka ta a frizer..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *