Buhari Na Dab Da Buɗe Boda-Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce ta yiwu Gwamnatin Tarayya ta sake buɗe kan iyakokin ƙasar kwanan nan.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya rufe kan iyakokin ƙasar a watan Oktoba, 2019, da nufin hana shigo da kayayyaki da makamai zuwa Najeriya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma nufin bunƙasa kasuwancin cikin gida.

Sai dai rufe kan iyakokin ya sha suka daga ƙungiyoyin ƙwararru, masana tattalin arziƙi da ɗaiɗaikun mutane.

Shugabanni ƙasashen Afirka kamar Ghana da Jamhuriyar Benin sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya sake duba matakin rufe kan iyakokin, amma Shugaban ya ce kan iyakokin za su ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da gwamnati za ta duba rahoton ƙarshe na kwamitin da ta kafa kan sha’anin boda.

Shugaba Buhari ya ce ƙasashe masu maƙobtaka su ma ya kamata su jajirce wajen hana shiga da kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba a ƙasashensu.

Sai dai lokacin da yake amsa tambaya game da ci gaba da rufe kan iyakokin da gwamnatin Nijeriya ke yi musamman a lokacin da Yarjejeniyar Kasuwanci Ba Tare Da Ƙaidi Ba Ta Afirka, AfCFTA, ke dab da fara aiki, Mista Osinbajo ya ce Najeriya tana aiki da maƙobtan ƙasashe a kan sharaɗan sake buɗe kan iyakokin.

Mista Osinbajo, wanda ya bayyana haka a yayin wani taron ƙara wa juna sani nda wata cibiya mai suna The Africa Report ta shirya a Intanet mai taken: Farfaɗowa: Shirin Najeriya na Farfaɗowa Bayan Annobar Corona”, ya bayyana cewa: “Muna aiki da maƙobtanmu don mu ga a bisa wane sharaɗai za mu sake buɗe kan iyakoki. A yanzu, muna yin sintirin haɗin gwiwa a kan iyakoki don magance shigo da kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba a kan iyakokin kuma muna tunanin hakan yana aiki, kuma ina da tabbas kwanan nan za mu sake buɗe kan iyakokin.

“Muna son aiwatar da AfCFTA, amma muna da damuwa game da barazana ga tsaro da tattalin arziƙi, kuma ya zama dole mu ɗauki wasu matakai da za su biya buƙatun ƙasarmu. Da ma rufe kan iyakokin ba a yi shi ne ya zama na din-din-din ba, kuma nan gaba kaɗan za mu sake buɗe kan iyakokin”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *