Babu hannuna akan fostar da aka haɗa hotona da Kwankwaso – Peter Obi

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2019 Peter Obi, ya ce ba shi da hannu a fostar da aka haɗa hotonsa da na tsohon gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso don neman takarar shugabancin kasar.

Fostar wadda ake yaɗawa a shafukan intanet, ta nuna cewa Peter Obi yana neman shugabancin Najeriya yayin da Kwankwaso yake neman mataimakin shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

A cewar fostar manyan ‘yan siyasar biyu suna takara ne a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, babbar jam’iyyar hamayyar ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce : “ba ni da hannu fostar da ake yaɗawa.”

Bai yi ƙarin bayani ba sai dai mutanen da suka yi tsokaci a saƙon nasa sun yaba kan yadda ya fito fili ya nesanta kansa daga fostar.

Ya zuwa wannan lokaci dai, tsohon gwamnan Kano Sanata Kwankwaso bai ce komai game da fostar ba.

Mista Obi ya tsaya takarar mataimakin shugaban Najeriya a lokacin da Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fafata da Shugaba Buhari a zaɓen 2019.

Tsohon gwamna Kano Kwankwaso kuwa ya fafata da Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar PDP wanda Atiku ya yi nasara.

Masu lura da lamuran siyasa na ganin Sanata Kwankwaso da Atiku Abubakar za su so Jam’iyyar PDP ta tsayar da su takara a zaben 2023 musamman sakamakon zargin da suke yi cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza cika alkawuran da ta yi na inganta rayuwar ‘yan ƙasar – zargin da ta sha musantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *