Ba A Naɗani Sarki Ba – Yariman Zazzau

Mai girma Yriman Zazzau, Alhaji Manniru ya nesanta kan sa daga wasu rahotannin da suka ce gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i ya nada shi sabon Sarkin Zazzau.

Yariman ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da wakilinsa, Santurakin Zazzau, Alhaji Surajudden Balarabe Yakubu ya fitar a daren yau Lahadi.

Ya ce; “A madadin mai girma Yariman Zazzau, Ni Surajudden Balarabe Yakubu, Santuraki Babba na Zazzau, ina so in jayo hankali ‘yan uwa da abokan arziki da masoyan Yarima cewa Dan Allah dan annabi a yi hattara kuma a lura cewa irin labarai da ake yada wa ta yanar gizo-gizo da kuma bidiyoyi da ake yadawa wai sun faru jiya ba gaskiya bane.”

A yanzu lokacin da nake maganar nan, yau lahadi da karfe bakwai da arba’in, har ila yau, gwamnatin jihar Kaduna ba ta bada sanarwar sakamakon muhawarar da suka yi akan zaben Mai martaba Sarkin Zazzau ba. Allah ne kadai ya san wadanda suka yi wannan makircin ko su waye suka yi.

Babu gaskiya a cikin wannan abin. Mu dai cigaba da addu’a, Allah Ya bamu nasara, Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *