Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Zulum

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum da ya yi sanadin rasuwar jami’an tsaro da wasu ‘yan civilian JTF.

An tabbatar da mutuwar a kalla jami’an tsaro 11 a harin na ranar Juma’a, wanda shine na biyu da aka kai wa tawagar Zulum a jiharsa.

A sanarwar da ta fito daga kakakin shugaban kasa Garba Shehu, shugaban kasar ya ce harin da aka kai a hanyar Maiduguri – Baga wani mataki ne na hana mayar da ‘yan gudun hijira gidajensu.


“Cikin alhini bisa rasa rayukan da aka yi a tawagar gabannin mayar da ‘yan gudun hijirar gidajensu, Buhari ya yi wa iyalai da masoyansu jaje,” .


“Shugaban kasar ya shawarci gwamnatin Borno da ke aiki tare da hukumomin tsaro da tattara bayannan sirri da kada su karaya game da aikin da suka sa a gaba na ceto garuruwan daga ‘yan ta’addan Boko Haram.”

Shugaban kasar ya kuma bukaci hukumomin tsaro da na tattara bayannan sirri su kara kwazo wurin samar da tsaro a hanyoyin da ke jihar.


“Shugaban kasar ya yabawa jarumtar jami’an tsaron da suka fafata da ‘yan ta’addan da kuma kokarin Gwamna Zulum da ke aiki tare da sojoji domin kawo karshen ‘yan ta’addan, sake ginin gidaje da kuma mayar da ‘yan gudun hijira gidajensu,”.


“Ya yi addu’ar Allah ya jikan jami’an tsaro da ‘yan sa kai na JTF da suka rasu ya bawa iyalansu hakurin rashi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *