Yadda El-Rufa’i Ya Duƙufa Wajen Zaɓen Sabon Sarkin Zazzau

Masu zaɓen Sarki a Masarautar Zazzau sun miƙa sunayen mutum uku ga Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i don ya zaɓi sabon Sarkin Zazzau daga ciki, a cewar wani rahoto na jaridar Daily Trust.

Rahoton ya ce masu zaɓen Sarkin sun miƙa sunan Iyan Zazzau, Bashir Aminu, wanda yake da maki 89; Yariman Zazzau Munir Jafaru, mai maki 87, sai Turakin Karamin Zazzau; Aminu Shehu Idris mai maki 53.

A halin yanzu, mazu zaɓen Sarkin suna ganawa da Gwamna El-Rufa’i a Sir Kasim Ibrahim Government House, Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna El-Rufa’i ya ce a halin yanzu yana karanta littafi na biyu wanda yake ƙarin haske a kan kan yadda aka zaɓi Sarkin Zazzau, Sarki Jafaru a 1937.

Gwamnan ya ƙara da cewa ya duba wasu takardu na sirri a kan yadda aka zaɓe Sarki Jafaru, da kuma yadda aka zaɓi Sarki Shehu Idris.

“Ina jiran shawara daga Kwamishinan Masarautu bayan jami’an tsaro sun tantance masu son zama Sarkin.

“A sannan ne zan iya zaɓar sabon Sarkin Zazzau. Don Allah a taimake ni da addu’a”, in ji Gwamna El-Rufa’i.

Masu zaɓen Sarkin sun karɓi buƙatar zama sarki daga mutum 11 waɗanda suka fito daga gidaje huɗu masu mulkin Zazzau don gadon kujerar marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu ranar Litinin.

Gidajen huɗu da suke mulkin Zazzau su ne:
Gidan Barebari
Gidan Katsinawa
Gidan Mallawa
Gidan Sullubawa

Gidan Barebari ya samu sarakuna tara, Gidan Katsinawa da Gidan Mallawa sun samu sarakuna huɗu kowannensu, sai Gidan Sulluɓawa da suka taɓa yin sarauta sau ɗaya kawai.

Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu, wanda shi ne shugaban masu zaɓen sarki, shi ya jagoranci zaman zaɓen masu son zama sarkin.

A cewar rahoton na Daily Trust, sauran masu zaɓen Sarkin da suka halarci taron su ne Fagachin Zazzau, Umaru Muhammad, Makama Karamin Zazzau, Muhammad Abbas, Babban Limamin Zazzau, Dalhatu Kasimu Imam da Limamin Konan Zazzau, Muhammad Sani Aliyu.

Gwamn El-Rufa’i ne zai zaɓi mutum ɗaya daga cikin sunayen mutum uku da aka miƙa masa don zama Sarkin Zazzau na gaba, kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *