Ra’ayi: Dimokraɗiyya ta zubar da ƙimar masarutun gargajiya a Najeriya

Tarihi ya tabbatar da cewa bayan jihadin Shehu Usman Bn Fodio, masarautu a kasar Hausa musamman wadanda Shehu ya bai wa tuta suna karkashin shugabancin daular ce, wato ayyukansu da tsari na shugabancinsu kamar naɗa sarki ko cire shi yana tabbata ne tare da sahalewar Fadar Sarkin Musulmi da ke da hedikwatarta a Sakkwato.

Haka abun ya ci gaba har zuwan Turawan Mulkin Mallaka wadanda suka sauya wannan tsarin ya dawo karkashin ikonsu.

Ina so ne na jawo hankalin mai karatu ya fahimci yadda ƙarfin ikon masarautun yake raguwa har zuwa wannan lokaci da ake ganin ƙarfin masarautun ya faɗi warwas.

A zamanin da suke ƙarƙashin Daular Sarkin Musulmi, ana naɗa sarki ne a bisa cancanta da alaƙa ta asali da gadon sarautar.

Haka Turawa suka ci gaba da yi a lokacinsu, wato a duk lokacin da sarki ya mutu, masu zaben sarki za su tura wa gwamna waɗanda suka tantance a cikin masu neman sarautar, shi kuma zai zaɓi wanda ya ga ya fi dacewa ya amince da naɗinsa a matsayin sabon sarki.

Wannan tsari ya ci gaba da tafiya har bayan samun ƴancin kai da kuma zuwan mulkin soja a ƙasar nan.

Daga shigowar mulkin jamhuriyya ta huɗu; matsayin sarakuna musamman naɗi da cire sarki ya zama abu me sauki a wajen ƴan siyasa, ta yadda son zuciya ya shigo cikin lamarin da ba a saba gani ba.

Duk da cewa cire sarakuna ko nada su sun faru a waɗancan zamani, amma ba su yi lalacewar da sukayi a wannan ƙarni ba; ta yadda gwamnoni ke cire sarakuna kamar yadda suke cire masu rike da muƙaman siyasa kamar yadda kuma suke naɗa wanda suke so ko da akwai wadanda suka fishi cancanta.

Hakan ya sa sarakuna suna nuna biyayyarsu wa gwamna, ko da kuwa zai saɓa wa al’ada da buƙata ta masarautar da kuma jama’ar da suke mulka, ta kai ma har zuwa kan hakimai da dagatai, wato sai wadda yan siyasa ke so ko suke ɗasawa dashi ne kawai zai iya samun sarauta.

Wannan al’amari ya jawo zubewar martabar masarautun a idon talaka, ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.

Abunda ya rage wa sarakuna a arewa shi ne kwalliya da hawa ƙasaitattun dawakai ana bikin hawan daba don burge mutane da ƴan yawon bude ido.

Fatanmu a nan shi ne Allah ya sa ka da mu wayi gari wata rana mu ji za a fara jefa ƙuri’a wajen zaben sarki da ya haɗa da ƴan takarar da ma ba su gaji sarautar ba.

Aminu Makama Ilelah, mai sharhi ne kuma malami a Jami’ar ATBU da ke Bauchi, Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *