Hon. Abdullahi Ya Kaddamar Da Shirin Horas Da Matasa Maza Da Mata 1000 Sana’o’i Daban-daban Don Dogaro Da Kai

Hon. Abdullahi Idris Garba (AIG), memba mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a Majalisar Wakilai ya kaddamar da shirin horas da mata da matasa fiye da 1000 a sana’o’i daban daban don dogaro da kai.

Dan Majalisan ya bayyana Shirin kaddamar da yin hakan ne a shafinsa na musamman na Facebook.

Dan Majalisa Abdullahi kamar ya Yadda ya bayyana a shafin nasa ya ce Shirin ya kashi kashi 6 ne inda ya ce a kowane kashe za a dauke matasa maza da mata 166 don horas da su sana’o’i daban daban.

Sana’o’in da za koyar da su sun hada da koyon takalmi, koyon sana’ar harkar zuma, kiwon kifi, kiwon kaji, koyon hada ‘yan kunne, abun wuya da sarkoki, da kuma yadda ake ajiyar abinci a zamanance.

Dan majalisa ya bayyana cewa da zaran sun kammala tantance wadanda za su ci moriyar wannan Shirin za a fara horas da su a nan take ba tare da bata lokaci ba.

A karshe kuma dan majalisan ya bayyana cewa bayan an kammala wannan shirin za a ba kowanne daga cikin matasan za a basu kudaden tallafi domin soma nasu sana’o’in wanda aka horas da su.

Ga hotuna a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *