Wani Ɗan Pakistan Ya Saya Wa Matarsa Fili A Duniyar Wata

Wani mutum ɗan Pakistan ya saya wa matarsa fuloti a duniyar wata, sakamakon samun hikimar yin haka da ya yi daga jarumin finafinan Indiya wato Bollywood, marigayi Sushant Singh Rajput.

Sohaib Ahmed, mazaunin Rawalpindi, ya sayo filin da yake a duniyar wata a wani yanki da ake kira “Sea of Vapour” a kan kuɗi dalar Amurka $45, kimanin N17,489 daga Hukumar Hadahadar Filaye A Duniyar Wata Ta Ƙasa Da Ƙasa, wato International Lunar Lands Registry, a cewar jaridar Intanet, Times Now News.

Mista Ahmed ya ce ya samu hikimar siyan fuloti a duniyar watan ne daga ɗan wasan Bollywood, Sushant Singh Rajput.

Filin da Mista Rajput ya siya a 2018 yana wani ɓangare da ake kira “Mare Muscoviense”, ko the “Sea of Muscovy”.

Fitattun jaruman finafinai na Indiya da suka haɗa da Tom Cruise da Shah Rukh Khan sun mallaki filaye a duniyar wata.

Matar Mista Ahmed, Madiha ta ce ƙawayenta ba su yadda ba lokacin da ta ba su labarin wannan kyauta ta musamman da mijinta ya yi mata.

“Da farko, kowa ya yi tunanin wasa ne, amma sai na nuna musu takardu sai suka yadda”, ta faɗa wa Gidan Talabijin na Samaa haka.

Ta ƙara da cewa wata ƙawarta ita ma tana son wanda zai aure ta ya ba ta kyautar fuloti a duniyar wata idan bikinsu ya tashi.

Mista Ahmed da matarsa sun karɓi takardun siyan fulotin a gidansu ta hanyar Hukumar Aika Saƙonni Ta Amurka, wato US Postal Service.

Tun farko, wani ɗan kasuwa mazaunin Bihar ya sayi fili mai faɗin kadada ɗaya bayan da shi ma ya samu hikimar yin haka daga Mista Rajput.

Neeraj Kumar, mazaunin Bodh Gaya, ya ce kuɗin siyan filin ba su yi yawa ba, amma tsarin sayan filin yana da wahala.

Ya tuntuɓi wata hukuma a Amurka mai suna “Luna Society International”, inda ya miƙa buƙatarsa ta siyan fulotin tun a Oktoba, 2019.

“Na bada kusan Rs 48,000 a lokacin, an mayar da kuɗin zuwa dala daga rupee, bayan yin aikace-aikacen takarda da yawa ta Intanet, sai na samu saƙo ranar 4 ga Yuli, 2020 cewa an kammala komai”, in ji Mista Kumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *