Babban Hafsan Sojin Saman Kasar Nan Ya Angwance Da Minista Sadiya Farouk

Wasu rahotanni daga birnin tarayyar Abuja sun bayyana cewa Babban hafsan sojin saman kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar ya angwance da Ministar Agaji da Ci Gaban Al’umma Sadiya Umar Farouk. 

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust an ɗaura auren ne a ranar 18 ga watan Satumbar nan da mu ke ciki a masallacin juma’a da ke unguwar Maitama da ke birnin tarayya Abuja. 

“Tabbas gaskiya ne shugaban sojin saman kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar ya angwance da Ministar Agaji da Ci Gaban Al’umma Sadiya Umar Farouk” daya daga cikin majiyar

“Sai dai mutane ƙalilan ne su ka halarci ɗaurin auren, saboda angwayen da kuma makusantan su ba sa son a yayata ɗaurin auren”

“Sun ɗauki lokaci suna soyayya wacce ta kai su ga zama ma’aurata, wanda hakan ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake akan soyayyar ministar da kuma shugaba Muhammadu Buhari”

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Oktobar shekarar 2019 ne aka samu wasu rahotanni da ke bayyana cewa shugaban ƙasa Buhati ya angwance da ministar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *