Rasuwar Sarkin Zazzau: Jarrabawa Ce Ga ‘Yan Najeriya – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya taimaka masa a lokacin yana shugaban kasa. Inda ya taimaka mishi ta hanyoyi da dama ta fuskar bada shawarwari, nashi da sanin dabarun mulki.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba a Zaria, jihar Kaduna yayin addu’ar uku da aka shirya don marigayi Sarkin a fadar Zazzau.

Ya kara da cewa marigayi Sarkin ya taimaka masa sosai a lokacin yana shugaban kasar Najeriya. Tsohon shugaban kasar ya ce: “Ya taimaka min wurin tafiyar da harkokin kasar nan. “Na tuna lokacin da rikicin Plateau ta taso. Bani da wanda zai taimaka min wurin yin sulhu a kan rikicin da aka dade ana yi, sai na kira shi, kuma ya sanya ni a hanya mafificiya.

“Marigayi sarki mutum ne mai son zaman lafiya da sulhunta mutane; mutum ne wanda baya nuna banbancin na addini, kabila ko matsayi na rayuwa.”

A jawabinsa, gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta yi rashin mai bada shawara kuma abin dogaro. “Gwamnatin jihar Kaduna ta amfana da shawarwari da hikima irin ta sarki saboda ya yi aiki da gwamnoni 20 da suka shude a jihar Kaduna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *