Zaben Edo: Buhari Adalin Shugaba Ne Wanda Ba Ya Ƙarfa-Ƙarfa – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari adali ne wanda bai taba yin amfani da kujerar shi ko isarsa ta hanyar da bata dace ba.

El-Rufai ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, wanda PDP ta yi nasara akan APC.

A yayin jawabinsa a shirin Sunrise Daily, wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce ya yi fatan APC za ta ci zaben. Kamar yadda yace, alamu sun nuna cewa jam’iyya mai mulki ce za ta yi nasara har sai a makonni uku da suka gabata.

“Ba kamar sauran gwamnatoci da suka gabata ba, Buhari yana bari a bar zabin jama’a a yayin zabe. “Mun so yin nasara. A gaskiya ina ta mana fatan nasara tare da sa rai har sai a makwanni uku da suka gabata.

A wani labari na daban, Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya fitar da takarda bayan lallasa shi da Gwamna Obaseki na jam’iyyar PDP yayi a zaben da ya gabata. Obaseki ya samu kuri’u 307,955 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri’u 223,619.

A martanin da ya fitar bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da nasarar Obaseki, Ize-Iyamu ya mika godiyarsa ga magoya bayansa a kan kokarin da suka yi masa yayin zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *