Zaɓen Edo: Talakawa Sun Kunyata Masu Maguɗin Zaɓe – Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki murnar lashe zabe karo na biyu da yayi a karshen makon daya gabata. Kwankwaso ya wallafar hakan ne a shafinsa na Twitter.

Kwankwaso yace , “Mutanen kirkin jihar Edo sunyi magana. Mutane sun nuna zabinsu na gaskiya. Don haka, inaso inyi amfani da wannan damar domin taya mutanen jihar Edo murnar gama zaben gwamnoni lafiya, kuma cikin kwanciyar hankali.”

Ya kara da cewa, “Inaso in taya mutanen jihar Edo murna musamman saboda tsayuwa da dagewa wurin kara zabar jagora mai dagewa wurin yin aiki tukuru, don ya cigaba da ciyar da jihar Edo gaba.

“Ina taya mai girma Gwamna Obaseki murna akan nasarar da ya samu, duk da dama ya cancanta. Yayi aiki tukuru ga mutanen jihar Edo, kuma sun nuna godiyarsu wurin kada maka kuri’u masu yawa.

“Sun kara da tsayuwa tsayin-daka saboda tabbatar da yan magudin siyasa da suka zo daga bangarori daban-daban basu samu nasara ba.

“Wannan zai kara bai wa duk wani dan Najeriya kaimi. Babu shakka, shugaban kungiyar kamfen na PDP, mai girma Nyesom Wike na jihar Ribas da duk wasu yan kungiya sunyi kokari matuka, kuma sun jajirce kwarai wurin ganin nasarar nan ta tabbata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *