Amfanin Dabino Ga Lafiyar Dan-Adam

Shi dai wannan dan itaciya ba bakon abu ne ba ga masu karatu. Kuma mun san cewa shi dabino ya sha bam-bam wajen girmansa, launinsa da kuma dandanonsa (zakinsa). Ana cin danye ko busasshen dabino,gwargwadon bukata. Ko dai a wanne irin yanayi akai amfani da shi ya na dauke da sanadarai masu matukar muhimmanci ga lafiya.

Mafi yawan mutane suna cin dabino ne don zakinsa, ba tare da sanin amfaninsa ga lafiyarsu ba. To sai dai dabino na da matukar fa’ida ga lafiyarmu.

Binciken masanan zamani ya nuna yawan cin dabino ga maza yana kara musu karfin sha’awa da kuma karfin mazakuta. Wasu masana sun shadawa jaridar Premium Times cewa yin amfani da dabino ga maza na kara musu karfin sha’awa da kuma karfin mazakuta. Dr Aminu Kareem ya shaidawa jaridar cewa, yawan cin dabino ga maza da ke da matsalar gamsar da iyali, na iya magance musu wannan matsala.

Saboda haka ne, mu ke son amfani da wannan dama don kawowa masu karatu irin dibim baiwar da ALLAH(S.W.T.) yai wa wannan dan itaciya ga lafiyar al’umma.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

  1. Karfin Mazakuta.

Kamar yadda muka fara ambatawa a sama, bincike ya nuna cewa dabino na kara karfin maza. Don samun sakamako mai kyau, a zuba dabino cikin nonon awaki ya kwana, sai a nike shi a hada da nonon da aka cire shi daga ciki a hada da zuma a sha. Hakanan a samu dabino kamar cikin tafin hannu,sai a cire kwallon a zuba a ruwa ya samu kamar awa biyu ko uku,a markade shi a zuba madara gwangwani daya da zuma cokali uku a sha sau daya a kullum.

  1. Cushewar Ciki.

Dabino yana magance cushewar ciki, saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira “Soluble fibre” a turanci. Shi kuwa wannan sinadari yana taimakawa wajen kewayawar abinci a cikin hanji cikin sauki.

Yadda za’a samu ingancin magance wannan matsala,a zuba dabino guda bakwai ko tara cikin ruwa su kwana a ci da safe.

  1. Karfin kashi.

Saboda dabino na kunshe da sanadaran selenium, manganese, copper da kuma magnesium ya ke kara karfin kashin dan adam. Su wadannan sinadarai da aka ambata a sama suna da matukar muhimmanci wajen ginin kashi.

Abu ne sananne cewa a lokacin da mutum ke kara manyanta kashinsa na kara rauni, don haka cin dabino akai-akai zai taimaka wajen ginawa da kuma kara masa karfin kashi.

  1. Gina Jiki.

Kasancewar sa yana kunshe da sinadaran suger, proteins da kuma nau’ikan vitamins yasa shi taimakawa wajen ginin jiki. Yawan cin dabino gami da kokumba na bada sakamako da sauri.

  1. Karin Kuzari.

Masana sun tabbatar da cewa dabino na dauke da nau’ikan suger kamar glucose, fructose da sucrose, wannan ya sa shi zamowa dan itace mai matukar amfani wajen karin kuzari. Saboda haka ne ma ya sa mutanen da suka fahimci hakan su kan ci dabino da zarar sun ji alamun kasala.

Haka nan ma mutanen da su kai aikin karfi ko motsa jiki suka gaji,suke cin dabino don samun wartsakewa da gaggawa.

  1. Lafiyar Zuciya.

Dabino na kunshe da sanadarin da ake kira potassium da turanci, wanda bincike ya nuna cewa yana rage hadarin bugawar zuciya, dama sauran cututtukan da suke shafar zuciya.

Don samun biyan bukata a zuba dabino guda bakwai ko tara a cikin ruwa, a fitar a ci bayan awa uku sau biyu a mako.

  1. Karfin Ido. Shi dai dabino na dauke da sinadarin vitamin A wanda ya ke taimakawa wajen kara karfin ido. Don haka sai a yawaita cin dabino don samun karfin ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *