Zaɓen Edo: Ba Mu Yarda Da Magudin Da INEC Ke Yi Ba – Oshiomole

Bayan bayyana nasarar jam’iyyar PDP a kananan hukomin takwas cikin goma sha biyu da INEC ta yi, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole ya ce ba za su amince da magudin da hukumar zabe take shirin shirya musu ba, domin babu adalci a ciki.

A wani lamarin daban kuwa kwamishinan zaben ya sanar da harbe wani jami’in INEC a karamar hukumae Etsako, sannan kuma wani jami’in tattara sakamakon zabe shi ma ya yi batan dabo a wata karamar hukuma.

Yayin da ya rage zaura sakamakon kananan hukumomi biyu da za a bayyana a hukumance, yanzu haka an tafi hutun awanni uku.

Zuwa yanzu dai Jam’iyar PDP ce a kan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *