Kotu Ta Tasa Keyar Wani Kansila Gidan Yari Kan Cin Zarafin Wani Dan Kasuwa

Kotun majistret mai zamanta a Airport karkashin mai shari’a Hajiya Talatu Makama ta aike da kansilan mazabar Bachirawa gidan kaso.

‘Yansanda ne dai suka gurfanar da kansilan Hon. Saddik Rabiu Zubairu, a kan zargin kansilan da lefin kutse da sanadin rauni da kuma keta alfarmar dan adam.

Kunshin zargin ya bayyana cewar, kansilan Bachirawa Saddiku Rabiu ya balle kofar shagon wani matashi mai suna Auwalu mai Wake ya yi masa dukan kawo wuka daga karshe kuma su ka hadu shi da wasu karti sun ja Auwalun a kasa sun sanya shi a but din mota sun kai shi ofishin Anti daba saboda mai waken yace wa kansila ya ci taliyar karshe.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ‘yansanda su ka gurfanar da su a gaban kotu amma da yake kotu wuri ne na adalci nan take mai shari’a Hajiya Talatu Makama ta bayar da belin kansila a ranar Juma’ar a ka kuma sanya yau Litinin domin a dawo kotu a ci gaba da shari’a.

Sai dai kansila bai samu damar halartar kotun ba sai bayan karfe 11 lokacin kuwa har an kirawo shari’ar sai dai a lokacin kansila bai karaso kotun ba.

Mai gabatar da kara ta roki kotun da ta karya belin tunda dai kotu ba ta jiran kowa sai dai a jira kotu kuma nan take kotun ta janye belin.

Yayin da kansilan ya bayyana a kotun ya nemi a yi masa hanzari kasancewar an wayi gari lauyansa baya jin dadi kuma shi ne ya kai lauyan asibiti sai dai kotun tayi watsi da rokon.

Tun da farko wanda ya shigar da kara Auwalu mai Wake ya bayyanawa kotun cewar, bayan kansila akwai wani dogarin kansilan mai suna Ado Babba da kuma kanin kansila Hassan Rabi’u wadanda suka yi masa wannan cin mutunci amma kuma kansilan kawai aka gurfanar, koda yake ‘Yansanda masu bincike kuma sune suka tsame wadancan mutane 2 ita kuma kotu abin da yake gaban ta shi take saurara.

Rahoton Dala FM Kano. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *