Ba Da Dadewa Ba Za A Dawo Aikin Umurah – Cewar Kasar Saudiyya

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin an dawo da gudanar da ibadar Umrah a ƙasa mai tsarki, tun bayan hutun da aka tafi sakamakon ɓarkewar annobar Korona.

Ministan aikin Hajji da Umrah Dakta Muhammad Saleh bin Tahir Benten ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake jawabi ta kafar yanar-gizo, domin sanar da kamfanonin jiragen saman da ke jigilar maniyyatan game da shirin da ƙasar ta yi.

Dakta Muhammad Saleh ya ƙara da cewa an yi tanadin matakan kariya daga yaɗuwar Korona domin daƙile yaɗuwarta a lokacin da za a koma aikin Umarar da sauran ziyarce-ziyarce na ayyukan ibada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *