Zaɓen Edo: PDP Ta Yi Wa APC Fintinkau

Jam’iyyar PDP ta sha gaban jam’iyyar APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo.
Hakan na nufin cewa dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben.
Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki;
Karamar hukumar Igueben
PDP: 7,870
APC: 5,199
Karamar hukumar Esan central
PDP: 10,964
APC: 6,719
Karamar hukumar Esan north-east
PDP: 13,579
APC: 6,559
Karamar hukumar Esan south-east
PDP: 10,565
APC: 9,237
Karamar hukumar Ikpoba Okha
PDP: 41,030 APC: 18,218 Karamar hukumar Owan east
PDP: 14,762
APC: 19,295
Karamar hukumar Etsako west
PDP 17,959
APC 26,140
Karamar hukumar Egor
PDP: 27, 621
APC: 10, 202
Karamar hukumar Esan west
PDP – 17,433
APC – 7,189
Karamar hukumar Uhunmwonde
PDP: 10,022
APC: 5,972
Jimilla: PDP: 171,805 APC: 114,730
Tazarar da ke tsakanin PDP da APC a halin yanzu: 57,075.
Ana sauraron sakamakon zabe daga sauran kananan hukumomi 8.