Bauchi: APC Ta Yi Babban Kamu

Tsohon Sanata dake wakiltar Bauchi ta tsaskiya Isah Hamma Misau a Jihar Bauchi, yayi ban kwana da Jam’iyyar PDP inda ya hada kai da Dogara a Jam’iyyar APC.

Tuni dai ruwa yayi tsami tsakanin Hamma Misau da Jamiyyar sa ta PDP da kuma gwamna Bala Mohammed dake jagoranci Jihar a halin yanzu, indai ba amanta ba Misau ya kasance a cikin yayan jam’iyyar da sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin sun kada Jamiyyar APC a zaben gamagari na 2015.

Kuma Jam’iyyar PDP har tabashi mukamin shugabanci kwamitin bankado al’mundahana da dukiyan al’ummar jihar, da suke zargin ta handame.

Bugu da kari aikin da yayi ma PDP a kasa da mako biyu shine, mai sa ido a zaben cikin gida na jam’iyyar PDP a Jihar Niger da ya gudana, kwatsam sai gashi jiya Jumma’a, ya karbi tutar Jam’iyyar APC a hannun shugaban ta na rikon kwarya Mai-Mala Buni kuma gwamnan Yobe a yanzu, to ko mai yayi zafi tambayara da yan jarida sukayi mashi kenan ta wayar tarho a garin Bauchi, sai yaka da baki, yana cewa” Siyasa kamar riga ce kowa da irin tasa, yace abinda jama’arsa suke gayamishi kenan, kuma gashi nayi hakan dominsu”

Sanata Hamma ya cigaba da cewa,” Salon yadda gwamnan Bala Mohammed Abdulkadir yake jagoracin jihar, baza su tsaya suna kallon sa kawai ba, bayan irin alkawurran da suka daukama al’ummarsu, cewa za a asamu chanji mai ma’ana, a wanan karo, to amma sai gashi yanzu ana zaton wuta a Makera sai gashi ta tashi a Masaka, yace gwamnan ya watsa masu kasa a ido”

Ya kara da cewa gwamnan ya maida mulkin jihar na yan’gida da abokanai kawai, shi yasa suka yake hukuncin bin tsohon kakakin majalisar dokoki ta tarayya Barrista Yakubu Dogara zuwa Jam’iyyar APC, inda suke ganin hakar tasu zata cimma ruwa.

Kana ya sanar da cewa akwai magoya baya kimanin su 50,000 wadanda zasu bisu zuwa Jam’iyyar APC a yankinsu na Bauchi ta tsakiya, Misau ya ce akwai wasu magoya bayan daga dukkanin kananan hukumomin jihar sun shirya tsaf don komawa Jam’iyyar APC.

Anashi martanin kuwa, Shugaban Jamiyyar PDP na Jihar Bauchin, Alhaji Hamza Koshe Akuyam yace,” ‘Ba giringirinba dai tayi Mai’ ‘me jiya ma tayi ballantana yau’ shugaban yace, shi kadai yazu a shekarar 2019 cikin Jamiyyarmu ta PDP, a lokacin da APC ta hana shi tikitin takaran shiga zabe, yace wanda ba ya iya cin zabe a akwatin zaben sa, irinsu in sukace zasu fita a PDP sai muce masu ‘Allah raka taki gona’” Ya karkare.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *