Zaben Edo: Sufeto Janar Na ‘Yan Sandan Najeriya ya Umarce Ni Na Bar Jihar Edo, Ni Kuma Na Ce Na Ƙi – Wike

Gwamna Wike ya ce Shugaban ‘yan Sandan Najeriya ne ya matsa min kan cewa ala tilas sai na bar jihar a daidai yau Asabar da ake gudanar da zaɓen Gwamna a nan Edo Ni kuma na ce masa na ƙi.

Wike ya faɗi haka ne a Tashar Talabijin ta Channel Tv a lokacin da yake zantawa da su inda ya cigaba da cewa wajibi ne in saka Ido a zaɓen domin Jam’iyya ta tayi Nasara kuma ina tsaye ne a matsayin Ɗan Jam’iyyar PDP ba Gwamna kawai ba, inji shi.

Matsayina na Shugaban Kamfen ɗin jam’iyya ta na ƙasa kuma gashi ba ni kaɗai na zo ba mun zo ne tare da wasu abokan aikina muna zaune a wani Otel kimanin ƙarfe 2 na Rana sai Sufeto Janar na ‘yan sanda ya kira ni cewa in yi maza in bar Jihar ni kuma nace masa Na ƙi.

Sannan sai na tambaye shi saboda me? sai ya ce mun saboda kasancewar ka a nan zai Iya Haifar da Yamutsi na sake tambayar sa Dan me? Sai ya ce mun ya ji a wurin kamfen ina cewa Jama’a su tsaya su kare kuri’un su kada su bari a yi musu murɗiya, Na ce na faɗa to meye laifi a nan?.

Bayan ‘yan Mintuna da basu wuce 10 ba kawai sai mukaji ƙarar motocin Jami’an tsaron ‘yan Sanda a ƙalla mun iya irga ‘yan sanda Sama da 300 a gaban Otel ɗin da nike kuma suka ce Umarni aka basu ba zan fita daga cikin Otel ɗin ba, Inji Wike.

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *