Jaruma Rahama Sadau Ta Cika Shekaru 7 A Kannywood

Tauraruwar Rahama Sadau ta fara haskawa a cikin Fim din ‘Gani ga wane’, a cikin shekarar 2013, wanda yau ke nan shekaru bakwai da fara fim a masana’antar Kannywood. 

Jarumar wadda fitacciya ce a cikin fina-finan Hausa na kannywood ta samu ɗaukaka a wannan harka domin ko a cikin shekarar 2018 sai da Majalisar Dinkin Duniya ta karrama Rahama Sadau. 

Lambar Yabo Da Ta Girma

Jaruma Sadau ta samu lambonin girma da yabo daban daban a kasar Najeriya dama kasashen ketare da dama wanda ya hada da Jaruma ta musamman a shekara ta 2014 da kuma 2015 wadda ta samu daga City People Entertainment Awards. Bugu da kari ta samu award din African Film Awards a shekara ta 2015 wanda African Voice ta hada.

Haka kuma a cikin shekarar 2018 sai da Majalisar Dinkin Duniya ta karrama Rahama Sadau. An karrama jarumar ne a wurin bikin ba da lambar yabo ta jaruman fina-finai mata Women Illuminated Film Festival, wanda aka yi a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.

Daga Kanywood zuwa Sana’ar Ƙwalan Da Maƙulashe

Sai dai a shekarar 2019 Rahama Sadau, ta raba kafa inda ta bude wani wajen ciye-ciye da shaye-shaye a garin Kaduna mai suna Sadauz’s lounge.

Hakan ya sanya jama’a ke ganin kamar Rahama Sadau ta raba kafa ne shi ya sa ta bude wannan waje, kasancewa ba kasafai ta ke fitowa a fina-finai ba a yanzu.

Kora Daga Masana’antar Kanywood 

A shekarar 2016 ne kungiyar masu shirya fina-finai ta ce ta dakatar da Rahma bayan da aka zargeta da rungumar wani mawaki a lokacin da ta fito a wata waka.

Wannan ya jawo suka matuka ga Rahama Sadau da Kannywood baki daya, inda akasarin jama’a ke nuna cewa abin da ta yi ya saba wa addininta da kuma al’adar Bahaushe.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a masana’antar Kannywood, abin da ya sa daga bisani jarumar ta bai wa magoya bayanta hakuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *