Uwa Ba Kashin Yadawa Ba, Uba Ba Kashin Yadawa Ba

Wani matashi Arakan wanda ya yi tafiyar daruruwan kilomitoci daga kasarsa zuwa Bangaladesh ta hanyar rataya tsofaffin uwansa a bayansa, ya zama abin alfahari kana gagara misali a duniya ga baki daya.

Matashin ya goya mahaifansa wadanda suka tsufa sosai ,inda ya yi tafiyar mako daya gabanin ya cimma kasar Bangaladesh.Kuma ya yi hakan ne don ya kubutar da su da kaidin mabiya addinin Buddah na kasar Myanmar.

Duniya ta yi matukar jinjina masa game da namijin kokarin da ya yi,wanda ba a kasafai ake ganin irin wadannan matasa a yanzu.Saboda a yawancin lokaci, a yayin da bala’i ya kunno kai, kowa ta kansa yake, babu mai kawo wa wani dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *