Shekaru 2 Muna Buga Soyayya Ashe Matar Aurece – Inji Wani Saurayi

Mun hadu ne ta kafa Facebook. Bayan nayi rubutu akan wani nazarin dana yi game da zaman aure da soyayyan mutanen mu. Wannan ne a cewarta ya jawo hankalin ta har ta turo mini sako ta Inbox ɗina tana mini jinjina bayan ta yi mini sallama.

Mako guda da aika mini wannan sakon sai na sake ganin wani sakon kuma na gaisuwa. Da yake naga lokacin da aka turo sakon da safe ne ni kuma sai wajen goma na dare na shiga shafina, sai na amsa da gaisuwar da aka turomini da tunanin zuwa safiya zata gani.

“Ashe baka yi barci” sakon da ta sake turo mini kenan bayan da amsa mata wannan gaisuwn data turo. Nace mata banyi ba amma dai ina shirin yi. Ke kuma mai kike yi haka har yanzu baki yi barci ba ko baki zuwa aiki ne? Na tambaya ta. Tace tana zuwa amma ita gobe bazata ba shi yasa take hira da Kawayenta.

“Yaya aka yi matarka ta barka har karfe goma baka yi barci ba.” ta turo da alamun mamaki.. Na amsa mata da tambayar ita ma yaya aka yi mijinta ya barta karfe goma bata yi barci ba. “ai ni bani da miji” to ai ni ma haka bani da mata. A wannan daren muka yi hira har zuwa 11 na dare kamin nan muka yi sallama.

Ina tashi da asuba bayan nayi sallah na kunna wayata sakon ta na soma gani na barka da tashi tana mini kuma fatan alheri. Nima na aika mata da sakon godiya. Haka dai muka ci gaba da yin hira ta Facebook jife jife. Har na tsawon kamar watanni 6 sai wata rana naga ta turo mini lambar ta inda ta nemi na tura mata tawa lambar na kuwa tura mata kamar yadda ta bukata.

Kira na gani da wata lambar ban Santa ba. Na dauka sai naji ana “hello, hello,” na fahimci dai muryar mace ce. Na amsa mata nima da hello. “baka ji nane” ina jinki wacece. “baka ma san ko wacece ba. Ko dai baka yi saibin lamba ta dana turo maka ba”. Sori gaskiya ban yi amma dai na gane wacce ke magana yanzu. “OK, daman na kiraka ne na tambayeka ko zan iya kiranka anjima kamar karfe tara zuwa goma muyi hira” na amsa mata da babu damuwa sai kin kira.

21:45 agogon bangon dakina ya ke nunawa a wannan lokacin ne kuma naga wayata tana haskawa da yake na cire ta daga kara. Sai naga ita ce take kira na. Bayan mun gaisa munyi hiran harkokin rayuwa sai kawai naji ta sako mini da zancen soyayya.

“Nifa tunokacin da muka soma musanya gaisuwa a Facebook naji ina sonka. Duk da dai bana saka hotona a Facebook baka kuma taba ganina ba amma dai kai kayi mini kuma gaskiya so nake mu hadu” yau she kike son mu hadu kuma a Ina zamu hadu? Na tambayeta ta bani rana da wajen da zamu hadu da kuma lokacin da zamu hadu. Na bata tambacin haduwar mu muka yi sallama ta kashe wayarta nima na kwanta.

Kamin mu soma hira da ita daman na samu matsala da wacce zan aura, hakan nema yasa nayi wannan rubutun da yayi Sanadiyar haduwa ta da ita. Don haka na yanke shawaran idan mun hadu kuma ta yi mini zan maye gurbinta da wacce muka rabu.

Na isa wajen saura mintuna goma akan lokacin da muka yi alkawari. Da yake wajen mahadar tamu wajene na jama’a sosai. Saboda kanti ne na saida kayayyaki wato Mall. Sai kawai na samu waje na tsaya ta inda zan iya ganin shigowar kowa kuma idan ta bugo mini waya zai yi saukin kwatance.

Kamin na taso daman ta mini kwatance irin kayan dake jikin ta don haka tana buga mini waya ban ma dauka ba na gane ita ce. Hakan yasa na lanlaba ta bayan ta sai na taɓa ta tana waigowa sai ta ganeni.
Riƙe da hannunta nake har muka shiga shagon cin kayan marmari muka zauna. A lokacin ne fa na tabbatarwa kaina cewa na samu matar aure idan dai ana maganar kyau ne.

Macece mai kyau halitta, ba fara bace kuma ita ba baka bace. Doguwa ce ina iya hango girman nonuwnta daga shatin mayafi data yafa. Tanada wushirya, kuma tana da jiki amma bata yi irin tum din nan ba. Amma dai da alamun zata girmeni.


A wannan ranar munyi hirarraki sosai, cikin har da rayuwar mu. Ta sheda mini ta taɓa aure amma mijinta ya rasu. Shekarunta na haihuwa 29 ni kuma 26. Tana aikin jinya ne a wani asibitin gwamnati na jihar ni kuma ina aikin a gwamnatin jihar ne.

A wannan ranar na jaddada mata a shirye nake muyi soyayyar da zata kaimu ga aure, amma kuma na nuna mata cewa ina bukatar dan lokaci kamin na yi auren.

“Kada ka damu. Ni kaina ba sauri nake yi ba. Muddin dai zaka kasance dani kuma ka rike alkawari babu matsala. Kaga dai na girmeka, kuma na taba aure duk da yake ban haihu ba kada na tsaya jiranka kuma daga baya ka shigo mini da zance irin naku na maza”.


Ko kusa bazan yaudare ki ba. Ina sonki kuma daga yanzu dana ganki son ki ya mamaye ni. Don haka ta bangarena babu damuwa. Na tabbatar mata da hakan.

Abun da ta mini kamin mu rabu ne yasa tun daga wannan lokacin har zuwa lokacin da nake rubuta wannan labarin naji babu wata macen danake so irinta. Bayan munyi sallama za mu rabu ne sai kawai ta bukaci nayi mata kis. Cikin rawan jiki na yi mata. Har lokacin dana koma gida zuwa lokacin da barci ya kwashe ni ita kawai nake gani daji. Kuma daga wannan duk bayan kwana biyu zuwa uku idan ban je wajenta ba sai tazo wajena. Soyayya sosai babu wanda bai santa ba cikin abokai na da kuma yan uwana na kusa.

Sai dai a duk tsawon wannan lokacin ban taba zuwa gidansu ba. Sai dai ko na sameta a wajen aiki ko kuma ita ta zo wajen aiki na ko kuma gidana. Haka kuma idan zamu Kaita gida muna shiga layin da tace layin gidansu sai tace yayi nan.

Duk kokarin dana yi domin nasan ko mai yasa bata bari mu karasa kofar gidan su ya faskara. Dukkannin dalilan da take bani bana gamsuwa amma saboda ina sonta sai kawai na amince da haka.


Na kamu da sonta matuka har na ƙagu ta bani damar na gabatar da kaina a gidansu saboda muyi aure. Amma kullum da uzurin da take kawo mini wanda zata nemi na dan bata lokaci. Ganin irin soyayyar da take mini babu lokacin da zan bukaci ganin ta dare ko rana da bazata zo ba. Babu wani abu da zan nema bata bani ba, babu abunda zan hanata bata hannu ba. Wannan yasa nake da tabbacin bazata yaudareni ba.

An turani gajeren horon sanin makamar aiki na makwanni biyu a wata jiha. Wannan lokacin ne a tsawon kusan shekaru biyu da nake buga soyayyar da ita muka taɓa kasancewa bazan ganta ba. Sai dai duk dare sai munyi hira kamar na awa guda ta whatsapp kuma sai taji murya ta kamin ta kashe wayarta.

Ana sauran kwanaki biyu na dawo ne muna hira sai kawai ta ce mini “Kafa shirya kana dawowa zaka turo gidan mu kuma kada ka sa dogon lokacin da za a daura mana aure”. Ban san lokacin dana yi tsalle ina ihu ba saboda murna. Da yake sakon whatsapp ne ta tura mini. Nace bari na kira saboda na tabbatar ita ce ta tura mini wannan sakon. Ina kira bugu daya tak sai ta dauka. Wai da gaske kike wannan tex din da kika aiko mini. Na tambayeta. “Kwarai kuwa, da gaske nake. Shi yasa ma na fadamaka tun kamin ka dawo saboda ka shirya”. Gaskiya naji dadi sosai yau cikin farin ciki zan kwanta.


Tsabar zumudi da murna a wannan daren na samo wani hoton da muka dauka da ita da kyar. Sai da ma tayi magiya na goge saboda bata son daukar hoto. Na goge ashe ban goge wannan ba na barshi a wayata. Kawai na dauko nayi posting a Facebook ɗina ina cewa ni da amarya ta nan bada jimawa ba.

Ina tashi a lokacin dana soma karanta komait sai nayi arba da wani da yake tambaya ta mai ya hadani da matar aure. Sai nayi banza dashi. Can a gaba kuma na sake ganin wani yake cewa “wane kuma matar aure aka koma nema”. A wannan lokacin ne hankali na ya soma dawowa daga jikina. Sai da naga comments kusan guda 7duk suna ambato mini matar aure. Cikinsu kuma babu wanda na sanshi gaba da gaba. Sai dai kuma dukkaninsu gari daya muke. Ina Shirin zan rubutawa wani cikin su wanda muka fi yawan chat dashi sako kenan sai ga wani sakon ya shigo mini ta Facebook.
“Mutumina wannan da matar aure ce. Ko dai kama suke yi da wance ne ina kasan ta” wannan shine tambayar da ya mini. Ni ma na tambayeshi ko ya Santa ne. Yace mini kwarai kuwa ya santa. “Tsakanin gidan mu da gidan iyayenta gidaje biyu. Wanda yake binta abokina nane. Sunanta…… Tana kuma aure a….. Sunan mijinta….. Tana aikin asibiti a waje…..” Don Allah ko zan samu lambar ka ina son muyi magana sosai. Yace babu damuwa. Amma yana bani shawara na goge wannan post din dana yi saboda kada ya jawo mini matsala. Hakan kuma nayi.
Bayan ya turo mini lambar na kirashi kuma na nuna masa soyayya muke yi da ita kuma har shirin aure ma muke yi. Na kuma fadamasa dalilin dama yasa nayi wannan post din.

“Amma wannan matar ta cika makira. Wallahi matar aure ne. Daman mijin ya jima yana zargin tana neman maza a waje. Sun sha rigimi ya korota gida. Saboda yawancin lõkuta baya zama. Kuma gidanta ita kadai ce sai yar ta da ɗan ta guda namiji amma duk kansu suna zuwa makarantan kwana ne. Bari ma na tura maka hotunan su”.
Na rike waya ina ta mamakin wannan lamarin tamkar almara. Ya kuma turo mini hotunan yara su biyu da kuma wanda suka dauka su uku da ita da kuma wanda su hudu da mijinta da yaran suka dauka. Daga nan kuma yace shi dai ya fadamini gaskiya saboda yana yawan ganin rubuta a Facebook kuma yasan ni dan garin ne.
Mãsu karatu na shiga matukar rudu ba karami ba. Ga yadda muka yi da ita. Ga kuma labarin daya zo mini. Ina neman shawarar ku akan matakin da zan dauka.


Ina sauraren ku. Na gode

(ba ita bace a wannan hoton ba)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *