Karin Kudi Lantarki: Idan Kun Yi Hakuri Nan Gaba Kadan Dadi Na Zuwa – Gwamnatin Tarayya

A ranar laraba gwamnatin tarayya ta jaddada cewa nan gaba kadan yan Nigeria zasu fahimci manufar gwamnati na kara kudin wutar lantarki, laolu Akande, hadimin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta fuskar watsa labarai, ya roki yan Nigeria da su ci gaba da yi wa gwamnati uziri

  • A cewar sa, dukkanin wadanda suke samun wutar lantarki ta kasa da awanni 12, su sanar da gwamnati, zata dauki mataki akai

Laolu Akande ya kare gwamnatin tarayya biyo bayan cece kuce da mamaye kasar sakamakon karin kudin wutar lantarki, yana mai cewa komai zai koma dai dai nan ba da jimawa ba.

Akande, hadimi na musamman ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ta fuskar watsa labarai, ya yi amanna da cewa karin kudin zai amfani ‘yan Nigerian.

“Mutanen da muke yin yarjejeniyar da su a kwadago, suma yan Nigeria ne. Za mu tabbatar masu da hakan,” a cewarsa, yayin zantawa da Channels TV, a ranar Talata.

“Babban abun lura a nan shine makomar kasarmu a nan gaba; tunaninmu, gaskiyarmu, rukon amana da kuma jajurcewarmu. Muna da tabbaci yan Nigeria za su fahimci hakan.”

Ya yin da ya ke yin nuni da cewa kowanne dan Nigeria yana da kashi a gindinsa, Akande ya roki ‘yan Nigeria da su ci gaba da yiwa gwamnati hakuri.

Akinde yana da yakinin cewa karin farashin kudin wutar lantarki, shine mafi dacewa a wannan lokaci, ma damar ana so a kawo ci gaba mai amfani a Nigeria.

“Ya kamata ‘yan Nigeria su fahimci matakan kariya da shugaban kasa ya sanya masu, kuma su yi mashi uziri akan kuncin da hakan zai kawo,” a cewar hadimin.

Dangane da matakan da gwamnati ke dauka don alkinta kudaden haraji, ya jaddada cewa da yawan ‘yan Nigeria za su dawo ba sa biyan kudin wutar lantarki.

A cewar sa, dukkanin wadanda suke samun wutar lantarki ta kasa da awanni 12, su sanar da gwamnati, za ta dauki mataki akai.

“Shugaban kasa ya kuma ce dole a samar da wadatattun mitocin wutar lantarki a kasar, a yanzu zamu fara kawo mitoci miliyan biyar,” a cewar sa kafin sauran su biyo baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *