Ilimantar Da ‘Ya’ya Mata Shine Mafita A Garemu – Lamiɗo Sunusi

Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana matsayarsa a kan karatun ‘ya’ya mata wanda yace shine jigon cigaban kowacce al’umma.

Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin kaddamar da wani sabon shirin cigaba ga malaman makaranta a kasar nan. Ya yi bayanin cewa shirin zai samar da damar inganta ilimi tare da bai wa mata da kananan yara damar samunsa a yankunan da rikici yayi kamari.

Ya bayyana cewa, shirin ya samu tallafi daga kasar Canada domin inganta neman ilimi tare da bai wa marasa karfi damar samunsa.
“Ilimi shine mabudin cigaban kowacce al’umma. Dole ne mu cigaba da bashi fifiko saboda shine jigon komai.

“Muna daga cikin al’umma masu yawa, farin cikinmu, nasararmu da cigabanmu ba zai yuwu ba sai da ilimi.
“Ina da tabbacin cewa ilimantar da ‘ya’ya mata zai kawo karshen mace-macen kananan yara, talauci kuma ya samar da ingantacciyar rayuwa ga al’umma,”

Sanusi wanda shine babban shugaban jami’ar jihar Kaduna, ya ce malamai masu matukar kwarewa za su iya zama tushen cigaba kuma za su iya kawo sauyi a al’umma.

A wani labari na daban, Muhammadu Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya ce bashi da wani buri na fitowa takarar kujerar siyasa a kasar nan.

A yayin da zaben 2023 ke gabatowa, ana ta hasashen ‘yan takara da za su bayyana kafin zaben. A wata tattaunawa da basaraken ya yi da Arise TV a ranar Juma’a, Sanusi ya ce bashi da ra’ayin siyasa kwata-kwata.

Tsohon basaraken ya ce zai koma karantarwa a fitacciyar jami’ar Oxford da ke Ingila a watan Oktoba mai zuwa. Hukumar kwamitin cibiyar Afrika ta makarantar, ta amince da bukatar Sanusi na komawa karatun. Tsohon basaraken ya ce yana da niyyar komawa malumta, wanda daga nan ya fara rayuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *