Dan Majalisa Hon. Abdullahi Ya Yi Jimamin Rasuwar Kwanturolan Kwastam Muhammad Hadi Garba

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Abdullahi Idris Garba wanda talakawa suka sakawa suna MAI SOLAR, yayi jimamin rasuwar tsohon kwanturolan kwastam na hedikwatar Fadakwal a jahar Ribas, Muhammadu Hadi Garba, wanda ya rasu a kwanan nan.

Dan majalisan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook indi ya yiwa iyalan mamacin ta’azziyar wannan babban rashi da suka yi.

Tsohon kwanturolan ya rasu ne a gidansa dake birnin jahar Neja, Minna bayan ya dan yi fama da rashin lafiya.

Hon. Abdullahi Idris Garba ya ce ba Za’a a Taba mantawa Da mamacin musamman Sakamakon irin ci gaban Da ya kawowa kasar Najeriya a lokacin da yake aikin Kwastam.

Ya kara da cewa babu shakka wannan rashi ba rashi bane kawai Da ya shafi iyalan mamacin ba inda ya ce wannan rashi babban rashi ga ma al’ummar jahar Neja ga baki Daya.

A karshe Dan majalisan ya roki Allah ya jikan Tsohon kwanturolan sannan yafe masa duk kura-kuransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *