Bincike: Mata Sun Fi Sha’awar Maza Masu Gemu Da Gashin Baki

Wani bincike da masanan kasar Ostireliya suka yi  a baya-bayan nan ya nuna cewa mata sun fi sha’awar maza masu gemu da gashin baki.

Masanan na jami’ar Queensland sun raba wa wasu mata dubu 8520, hotunan mazaje masu gemu da gashin baki da kuma marasa su,inda aka tambaye su da su zabi namijin da suke ganin cewa ya dace su aura don samun zurri’a.

Sakamako ya nuna cewa kusan dukannin matan sun zabi mazaje masu yawan gemu da gashin baki a matsayin wadanda suka dace su aura.

Masanan sun ce barin gashin baki da gemu, na aika wa kwakwalwar mata wani signa wanda ke nuna musu cewa namijin da za su aura nutsatstse ne kana mai halin dattako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *