Yadda Ake Girka Farfesun Kaza Da Dankalin Turawa


FARFESUN KAZA DA DANKALIN TURAWA


Kayan Hadi:
►Kaza
►Dankalin
►Karas
►Curry
►Maggi
►Thyme
►Tattsai da tumatur
►Gishiri.


Yadda Ake Yi:

Da farko za ki feraye dankalinki ki yanka kanana, sai ki dauraye kazarki ki sulalata da maggi da tafarnuwa idan kina bukata da curry da themy da gishiri,sai ki jajjaga tattasai da tumatur da attaruhu,idan kika sulalasu sai ki zuba karas da kika kankare bayanshi ki yanka a ciki sai ki zuba aciki dankali ma ki zuba a ciki ki hada da kazar su dahu har lokacin da kike bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *