Shawara Zuwa Ga ‘Yan Mata A Kan Kulawa Da Tsabta

Ƴan Mata………

✍️Yayin da kike Al’ada “Period” kada ki bari aji kina tashi-tashi (Wari),domin hakan yana Zubar da Qimar ki.

✍️Idan kika ji warin ya wuce Misali to fa ki dangana ga Asibiti,domin wasu laluran na kawo Hakan.

✍️Kamar yanda kika saba kafin kiyi Bawali ko Ga’iɗi kina wanke Hannunki da sabulu,kafin kiyi tsarki sannan ki tsane ko ina da Tissue kafin mayar da pant,to idan kina Period shima duk bayan wasu awanni yana da kyau kije ki chanja pad da pant,sai dai shi anfi Son yayin da zaki chanja ki tanadi Ruwanki na ɗumi wanda kika sa Ɗan Gishiri,Ruwan me yawa kiyi dogon tsarki ki cuɗa ki wanke ko ina sannan ki tsane da tissue.

✍️Yana da kyau kafin sanya Pant da pad ko duk abin da kike amfani dashi na Qunzugu, idan da Hali ace kina da Miski da zaitun ɗinki ,ki shafa a matsematsin cinyarki da kan pad ɗin,sannan ki sanya bayan tsanewar,kana ki qara wanke Hannunki.

✍️Wasu suna fama da ciwon Mara,suyi qoqari su daina shan kayan zaqi,maiqo ,Yaji,sannan su dinga Tafasa yar tsamiya suna sha da Zuma a wannan lokacin,yana Taimakawa,musamman idan akwai zaitun Asha cokali 1 ko 2 kullum,wasu ma har sau 3,wanka sau 2 da Ruwan ɗumi dashan Ruwan ɗumin kansa, da chanja Tufafi yana Taimakawa.

✍️Yawaita Azkar a wannan lokacin yana da mahimmanci,domin Abokanan Rayuwar mu(Jinnu) suna Amfani da wannan damar sosai da sosai.

✍️Daga sanda kika kammala Haidha,ki Goge duk inda kika san Jinin ya taɓa da Miski da Audiga,Dangwala za kiyi sai ki gwaggoge,sannan kije Kiyi tsarki da wankan Tsarki kici gaba da Ibadarki ki,ci gaba da Ɗahara da Ruwan ɗumi,wanke duk wani Pant da kikayi amfani dashi ki tsaftace ki Adana ,sai kuma wani lokacin ki Ɗakko su,idan da hali Anso kici ƴaƴan Itatuwa ko wani abu dazai qara Miki jini da lafiya bayan gama Al’ada koda Ganye ne.

Allah yasa a dace.Ameen.

Aunty_Zuhra.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *