Mutuwa Ba Ta Barin Kowa

Allahu akbar Dan Adam:Tabbas wata rana sai labari, ‘yan uwa ina tuna mana cewa yadda mintutunan agogo ke wucewa ba dawowa haka wuni da kwanan mu ke wucewa, kuma kamar yadda numfashin mu da ke shiga da fita haka a hankali zai kare wata rana sai tafiya lahira.

In ajali yazo ba’a jinkirtawa kowa, don haka mu zauna cikin shiri da tanadi tafiyar da ba dawowa, kuma zuwan ta ba notice…

Ina rokon Allah yasa mu cika da imani, Allah muna rokon ka kar6e mu a lokacin da kafi yarda damu.

Abin so shine muna yiwa kan mu hisabi kafin ranar hisabin mu tazo, kuma muna tunani da tsammanin in mun wayi gari kamar ba zamu kai maraice ba, haka in dare yayi mu dauka kamar ba zamu wayi gari ba.

Yin haka zai karfafa zuciyar mu da yawan da’a, yasa muna yawan ambaton Allah, kuma mu rage dogon buri; da karanta aiyukan sa6o.

Mu lura fa ita mutuwa wa’azi ce wato tana karantar damu cewa in yau wani ya tafi, jiya ma sai mu tuna ai mun bunne wanin mu, tab gobe kuma zai yiwu ni zaku binne, in an dawo may be kai za’a raka makwanci..

Kabari ne zangon mu na farko nan zamu sha tambayoyi, ba kowa ciki sai aikin mu da halin mu.

Allah sarki dan adam yana ta hada-hada da kai kawo, Ana ta shirin rayuwa, wassu na ta rigima da kulle-kulle, ta hannun dama wassu na ta ibada da biyayya ga shari’ar Allah haka dai kwatsam sai mai raba masoya mai yanke jin dadi ta riske ke shi.. Lallai barin duniya ba Makawa; in tazo ba gurin 6uya.

Wallahi yadda kullum ake dare gari ya waye, kuma ake bacci a farka wata rana haka zaka koma ga Allah. Ranar da zaka wayi gari ba za’a kai dare da kai ba tana zuwa, ko ranar da zaka kai dare ba za’a wayi gari da kai ba.. ranar da hatta wanka sai an anyi maka, masoyan ka da kansu zasu tu6e ka su sa maka likkafani suje su binne ka da kansun…

Allah ya bamu dacewa yasa muyi sa’ar zuwa lahira, amin
M Aliyu Sai’d Gamawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *