Amfanin Ganyen Garin Magarya

Itaciyar magarya wadda akafisani da (Assidir) a larabce itaciyace mai albarka da daddeden tarihi, Tunkafin zuwan musulinci ana amfani dashi kuma bayan zuwan musulinci Annabi s.a.w ya tabbatar da amfaninsa duk da su turawan yamma sai afarkon karni na shatara suka sanshi.

Magarya yana kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma yana da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci magarya Antibiotic ne mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato side effects na azo agani.

KADAN DAGA CIKIN AMFANINTA.

 1. Ciwon daji (cancer) : Idan ana dafa garin magarya anasha da
  zuma yana kashe kwayar cutar daji koda nacikin jini ne idan
  kuma Yayi miki sai arinka dafa garin magaryar da ruwan khal
  ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbada garin magaryar.
 2. Yanada karfin yaqar cutar fata kamar su tautau, makero,
  Kanzuwa da sauransu sai A kwaba shi da zuma arinkasha Ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.
 3. Yana tsaftace jini domin Yana dauke da sinadarin
  Saponin,alkaloid da triterpenoid wadannan
  Sinadaraine masu tsaftace Jini.
 4. Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon
  Jiki.
 5. Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko
  zuma.
 6. Yana taimakawa hanta ya hanashi jin ciwo da cututtuka.
 7. Yana daidaita nauyin mutun.
 8. Yana tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Shashi da ruwa ko koko.
 9. Yana miqar da kasusuwa musamman ga mai karaya.
 10. Yana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki dashi kuma Suna shansa da madara. Wallahu
  Alalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *