Zulum ya amince Da Daukar Karin Ma’aikatan Lafiya 594 ga Asibitocin Jahar

Gwamnan Jahar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da daukar Likitoci guda 84 aiki da, malaman Jinya guda 365, da Kananan Ma’aikatan Lafiya gami da sauran Ma’aikata, domin karawa ga Bangaren Lafiya a Jahar.

Zulum ya bayyana daukar aikin a ranar Litinin din nan a Maiduguri, a Karshen taron da yayi da Masu ruwa da tsaki a bangaren Lafiya, wanda ya samu halartar Shugaban Kwamitin Majalisa na Jaha akan Lafiya, da Kwamishinan Lafiya Dr Salihu Kwayabura da Shugaban Kungiyar Malam Jinya gami da masu ruwa da tsaki, inda taron ya gudana a gidan Gwamnatin Jahar.

Gwamnan ya kara dacewa daga cikin Malam Jinya 365 daza’a d’auka, to rabinsu zai kasance wadanda Suka Kammala Makarantu bada jimawa ba, a sa’ilinda rabinsu kuma zai kasance wadanda suka ajiye aikine a Jahar a Matsayin Malaman Jinya, inda za’a basu kwantiragi.

Hakazalika likitoci 84, Gwamnan yace za’a dauki wasu a matsayin ma’aikatan din din din, inda wasu zasu kasance akan kwantiragi da Likitoci masu ziyara daga wasu jahohin.

Zulum yayi nuni dacewa ya kuma amince da daukar Ma’aikatan kula da Magani 45 da sauran Kananan Ma’aikatan wadanda zasuyi aiki a Sashen gwaje-gwajen da sauran a bangaren Lafiya.

Hakanan kuma, Gwamnan ya amincewa Makarantar Koyarda Jinya data kirkiro da wata gidauniya wadda zata bayarda dama ga Makarantar ta d’auki d’alibai 200 a duk Shekara a Makarantun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *