Yadda Mataimaki Na ya Ceci Rayuwata A Yayin Da Aka Yi Ma Ni Kwantan Bauna – Buratai

Shugaban Sojin Kasa Laftanar-Janar Tukur Buratai, ya bayyana yanda mataimakin sa Laftanar-Janar Lamidi Adeosun, Shugaban kula da horaswa da harkokin Rundunar, ya ceci rayuwarsa a dai-dai lokacinda aka yi mashi Kwantan ‘bauna a yankin Arewa Maso Kudu.
Buratai yayi jawabin a Kuta Jahar Osun, a lokacin kaddamar da Gada wadda aka sanya sunansa da Makarantar horasda kere-kere ta Hukumar soja tayi dake Ede.
A lokacinda yake Magantawa akan ayyukan Soji a Arewa Maso Kudu, yace a sa’ilinda aka nadashi Shugaban Soji, ya hadu da Adeosun, ‘Dan asalin Asamu ta Jahar Osun,
Wanda yace ya tayin kokari domin canja harkokin Soji.
Yace ” a lokacinda akayi man Kwantan ‘Bauna, to yana tare dani a cikin Mota, wanda ya faru a ranar 18 ga watan Satumba na Shekarar 2015, kuma naga irin kokarin sa”.
“ya kuma yi ‘ko’kari wajen hada runduna domin tunkarar yan ta’addan, a dalilin haka yan ta’addan suka ruga suka bamu hanya, to na dade ina ganin kokarinsa.
Dayake kara yin jawabi, Buratai yace makarantar jami’an Rundunar Soji bangaren kere-kere wanda suka gina Gadar nan, zai zama abin tarihi da tayi da kuma kokari domin bunkasa tattalin arziki a Kasar nan.