Sojojin Sun Kama Wasu Masu Safarar Miyagun Kwayoyi A Zamfara

Jami’an sojan operation Sahel sanity sun sami nasarar kama wani mutum tare da wata Mata wato Kabiru Dauda da Hafsat Musa ,Wanda aka samesu tare da jakunkuna guda 9 dauke da kayan maye da ake zargin tabar wiwi ne da sauran haramtattun abubuwa kamar kwayoyi.

Wannan bayani ya fitone daga bakin Mukaddashin Darakta,ayyukan yada labarai na hukumar Tsaro Birgediya janar BENARD ONYEUKO, a lokaci da yake yiwa manema labaru bayani kan nasarar da sojojin suka samu a kwanakin nan a faskari ta jihar katsina.

ya kara da cewa tun cikin Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne ga ‘yan fashi.

Hakazalika ya ce sojojin sun kama wani da ake zargi dan fashi ne wanda suka jima suna nema mai suna Usman Gorjo a Ungwar Alhaji Danbuzu da kuma wani da ake zargin shi ke kai rahotonni ga barayi mai suna Isah Bala a kauyen Daudawa.

Ya kuma bayyana cewa sojojin sun kama wadanda ake zargi da kisan shugaban kungiyar ‘yan banga na Daudawa a kwanakin Baya.

Ya ce sojojin sun Kai samame a yankin Shekewa sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda da dama tare da cafke wasu da ake zargi’ yan fashi ne su uku da Adamu Musa da Hassan Bello da Rabiu Salisu, shi kuma guda an kashe shi ne yayin da yake kokarin tserewa a kan babur.

Bugu da kari, sojojin da ke amsa kiran gaggawa sun dakile wani yunkuri Kai hari a kauyen Magami, ya ce lokacin da suka isa ƙauyen, yan fashin sun fafata da sojoji suka tilasta yan fashin suka tsere cikin rudani sai dai sun Kama wani mai suna Abubakar Umaru.

A wani mai Kama da wannan sakamakon samun bayanai daga mazauna yankin, sojoji sun cafke wani mai suna Yahaya Abubakar wanda aka bayyana shi da cewa dan kungiyar ta’addanci ne a kauyen Ungwan Kardorako,ya ce Wanda ake zargin yana tsare ana masa tambayoyi.

Ya ce kuma a ci gaba da aikin sintiri sojojin sun ci karo da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a kan hanyar Bindim-Magami, bisa blabura ,yace sojojin suka tilasta musu yin watsi da wadanda aka sace su uku, yayin da suka samu damar tserewa zuwa cikin daji da ke kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *