Kungiyar Arewa Media Writers Ta Gabatar Da Taron Tattaunawa Karon Farko A Matakin Kasa

Kungiyar marubutan Arewa a kafafen sadarwar zamani ta kasa wato “Arewa Media Writers” ta gabatar da taron tattauna wa a karon farko a matakin kasa, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, wanda ya gabata a jihar Kano.

Shugabannin Kungiyar daga dukkanin jihohin Arewa ne suka sami halartar taron wanda zai dau tsawon kwana biyu Kungiyar tana gabatar wa a cikin kwaryar jihar Kano.

An gudanar da taron ne kan yadda za’a kawo wa yankin Arewa cigaba domin bunkasa yankin, tare da kokarin dakile dukkannin labarun karyar da ake yakar yankinmu na Arewa.

Haka zalika Kungiyar tayi kira ga Al’umma da su bawa kungiyar hadin kai tare da goyon baya domin kawo wa yankin Arewa da Nigeria baki daya cigaba.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana bukatar Addu’o’i daga gareku Allah ya shige mata gaba kan muhimman ayyukansu da ta saka a gaba.

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *