Da Duminta: Allah Ya Yiwa Sarkin Biu Rasuwa

Allah Ya yi wa Sarkin Biu, Alhaji Umar Mustapha Aliyu, rasuwa ranar Litinin da dare bayan fama da rashin lafiya.

Iyalan mamacin sun tabbatar da rasuwarsa a garin na Biu, da ke Kudancin Jihar Borno, yana da shekaru 70.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

“Allah Ya yi wa Sarkin Biu Alhaji Umar Mustapha Aliyu, rasuwa.

“Ya Allah Ka ba wa iyalansa da daukacin mutanen Masarautar Biu hakurin jure wannan rashi. Hakika bango ya fadi.

“Allah Ya gafarta masa kurakuransa Ya kuma sanya shi a Aljannah Firdausi”, kamar yadda wani daga cikin iyalan ya shaida wa manema labarai

Haka kuma ana sa ran za a binne shi a fadarsa, ko da yake ana dakon sanarwar da Gwamnatin Jihar Borno game da rasuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *