ASUU: Jami’o’i Ba Za Su Taba Budewa Ba Har Sai Idan An Biya Mana Bukatun Mu

Kungiyar Malam Jami’o’i tayi kira ga Gwamnatin Tarayya data girmama bu’katunsu wanda tayi yarjejeniya da ‘Kungiyar, kafin Sanarwar bude Jami’o’i bayan wucewar Annobar COVID-19.

Kungiyar tace bazata bada damar bude makarantun ba idan Gwamnatin Tarayya taki amicewa, data tattauna da ita akan yarjejeniyar da aka cimmawa ta Shekarar 2009 wadda dukkaninsu suka rattaba hannu.

Dayake jawabi a dakin taro na Afirka dake Jami’ar Ilorin, Shugaban Kungiyar na Kasa Farfesa Biodun Ogunyemi, yaki bayyana ajendar kungiyar akan abinda ta dosa.

“Inaga yafi mujira mugani har sai munga mun cimma nasara, domin bazan iya bayyana matakan da zamu d’auka ba, sai idan Gwamnati taki amicewa ta tattauna da mu, a lokacin zamu bayyana abinda muka shirya” Inji Biodun

Ya bayyana cewa ‘Kungiyar ta tafi yajin aiki tun a watan Maris sakamakon rashin bada mahimmanci ga Ilmin Jami’o’i, inda ya kara dacewa wasu daga cikin bukatun Kungiyar sun hada da; Bayarda kudade domin tafiyar da Ilmin Jami’o’i.

“Akwai kwakwkwaran yunkuri na Kashe Ilmin Jami’o’i a kasar nan, domin wasu daga cikin jami’o’in Risho suke amfani maimakon kayayyakin zamani domin gudanar da bincike ” Inji shi.

Ya kara dacewa Kungiyar ASUU tayi yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya akan bukatar inganta kayayyaki a cikin jami’o’i , da suka hada da; ‘Dalibai, da jindadinsu da Ma’aikata, da Karin girma wanda aka banzatar ” domin a halin yanzu akwai tsare-tsaren sanya ilmi yafi karfin ‘ya’yan talakawa, wanda yin hakan ya kirkiro Ayyukan ashsha da suka hada da; ‘yan Yahoo-Yahoo, da ta’addanci gami da sauran ayyuka ta’addanci a cikin Al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *