Sojojin Najeriya Sun Kama Mayakan Boko Haram Da Dama (hotuna)

SOJOJIN NIGERIA SUNYI RAMUWAR GAYYA AKAN YAN KUNGIYAR BOKO HARAM DA YAMMACIN YAU LARABA.

Daga Kabiru Ado Muhd

Rudunar sojojin Nigeria ta operation zaman lafiya dole sun kashe yan kungiyar boko haram sama da guda Ashirin 20 kuma sun raunata wasu da dama, sannan sun kwato motar yaki Daga hannun yan ta addan a jihar borno.

Rundunar sojojin sun yiwa yan ta addan wani kwanton bauna ne yayin da suka bayanan sirri a lokacin da yan ta addan sukai shirin kawo wani mummunan hari garin bama.

Bukar sale wani dattijo dake sana ar saran itace ya bada labarin cewa yana cikin tafiya ya hangi wucewar gungun sojojin a guje har wasu Daga cikin sojojin suna nuna masa alama Daga nesa cewa yayi sauri ya koma baya hanyar bata da kyau.

Bukar sale yakara da cewa wucewar babu dadewa seya ringajin wuta babu kakkautawa.

Bukar yace be karasa inda ya dosa don tsira ba seya ringa ganin sojojin suna ta dawowa gawawwakin yan ta addan boko haram din Abin kyawun gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *